'Yan Bindiga Sun Buƙaci Kuɗin Fansa Da Sabon Naira Daga Comrd Yusha'u Garba Shanga Wasu ‘yan ta’adda da suka yi garkuwa da mutane h...
'Yan Bindiga Sun Buƙaci Kuɗin Fansa Da Sabon Naira
Daga Comrd Yusha'u Garba Shanga
Wasu ‘yan ta’adda da suka yi garkuwa da mutane huɗu da suka hada da namiji da mace da yara biyu a ƙauyen Kolo da ke ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
An tattaro cewa bayan sace waɗanda aka yi garkuwa da su, 'yan bindigar sun buƙaci a biya su Naira Miliyan (Goma) N10m, kuma tare da gindaya sharaɗin rashin amincewa da tsoffin takardun naira.
Wani ɗan asalin yankin mai suna Mohammed Ibrahim, ya ce daga baya ‘yan fashin sun rage kuɗin fansa zuwa Naira Miliyan (Biyar) N5m, inda ya ce mutanen ƙauyen sun yi ta ƙoƙarin tara kuɗin fansar domin a sako waɗanda lamarin ya shafa.
“A yayin da muke ƙoƙarin tattara kuɗaɗen da ‘yan ta’addan suka nema, sun sake aike da wani saƙon a safiyar yau cewa ba za su karɓi tsoffin takardun naira ba.
"Sun ce za su ci gaba da ajiye mutanen da aka sace a sansanonin su har sai an fitar da sabbin takardun Naira a watan Disamba," in ji Ibrahim.
Kiraye-kirayen da aka yi wa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya ci tura.
Har yanzu ba a amsa saƙonnin rubutu da aka aika zuwa lambobin wayarsu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
No comments