Amfanin lemin tsami 🍋 Yana da kyau idan ka karanta ka turawa sauran Al'umma. 1. Maganin Rauni. Sakamakon ayyukanmu na yau da kullum, m...
Amfanin lemin tsami 🍋
Yana da kyau idan ka karanta ka turawa sauran Al'umma.
1. Maganin Rauni.
Sakamakon ayyukanmu na yau da kullum, musamman mata dake mu'amala da wuka lokutan girki, ko kuma su mazan ma'abota aiki da wuka, idan bisa tsautsayi akai wani rauni ko yanka, yin amfani da lemon tsami ka iya warkar da shi cikin gaggawa. Idan haka ta kasance sai a matsa ruwan lemon a kan ciwon, zai kame ya kuma warke da yardar Ubangiji.
2. Taimakawa Ma Su Fama Da Basur.
Ga wadanda ke fama da cutar basur musamman wanda ake kira "Basur mai fitar baya" za su iya samun sauki ta hanya amfani da lemon tsami. Mutanen dake fama da wannan larura ana ba su shawarar gujewa cin abincin da zai haifar mu su da bayan gida mai tauri, saboda hakan ne ke sabbaba mu su tashin basur din. Shan ruwan lemon zai sanya bayan gidansu ya kasance mai laushi, wanda hakan zai haifar mu su da yin bayan gidan cikin sauki.
3. Magance ciwon gabobi da kuma ciwon cikin tsoka.
4. Samar da lafiyayyun hakora saboda sanadarin calcium dake kunshe a cikinsa.
5. Gyara hanyoyin numfashi sannan ya samar da riga-kafi daga kamuwa daga cutukan da kan shafi hanyoyin numfashi.
6. Inganta lafiyar Ido da samar da riga-kafin cutukan da kan shafi ido.
7. Hana yamushewa da yankwanewar fata.
8. Tamakawa hanta fitar da datti daga cikin dan-adam.
9. Warin Hammata.
Bai kamata ace mutum na mutane dake mu'amala cikin mutane a kowanne lokaci ya yi sakaci wajen barin hammatarsa na wari ba. Hakan zai haifar ma sa da kyama da zubar kima daga mutanen da ya ke mu'amala a da su. Domin gujewa hakan sai ya juri yin amfani da lemo. Zai yanka ne, sannan ya shafa a hammatarsa, bayan kamar mintuna 15 sai ya wanke.
10. Maganin Mura.
An tabbatar da ya na magance mura, musamman idan aka matsa ruwansa cikin shayi mai zafi a ka sha. Ana son a hada shi da danyar citta, da tafarnuwa sai a dandaka su sannan a matsa ruwan lemon a cikin shayin. A sha wannan hadi a kalla sau biyu a rana wato da safe sannan da yamma.
Kari kan wadannan fa'idoji da mu ka jero a sama, za a iya amfani da ruwan lemon amma a gauraya cikin ruwan dumi, a sha kofi daya kafin a karya da safe. Yin hakan zai iya magance.
GARGADI⚠️⚠️
Banda masu fama da gyambon ciki wato Ulcer.
Allah yasa mu dace.
Daga Maijalalaini Islamic medicine 08137482786 WhatsApp 0r Call 08088863000 daga 12 na rana zuwa 10 na dare.
Muna jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist muna budewa 12 na rana zuwa 8 na dare.
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :
Copyright BY: maijalalaini Islamic chemist
FACEBOOK GROUP: maijalalaini Islamic chemist
EMAIL: drmaijalalaini
FACEBOOK PAGE LIKE: maijalalaini Islamic chemist
WhatsApp: 08137482786
Domin shiga group na Telegram 👉 Telegram
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati
Share.
No comments