Wani Mutum da aka yi garkuwa da 'ya'yansa biyu a jihar Kwara yana neman sayar da gidansa cikin gaggawa domin ya biya kudin fansa ga...
Wani Mutum da aka yi garkuwa da 'ya'yansa biyu a jihar Kwara yana neman sayar da gidansa cikin gaggawa domin ya biya kudin fansa ga 'ya'yan nasa har Miliyan 8
Wani mutum dan asalin garin Aseyori ta Kwara mai suna Lukman Aliyu ya fara sayar da kadarorinsa domin ya hada kudi har Naira Miliyan 8 da 'yan bindiga suka nema domin su saki yaransa guda biyu da suka yi garkuwa dasu.
Jaridar SaharaReporters ta rawaito cewa Lukman Aliyu an sace yaran nasa masu suna Muhideen Lukman da Abdulkadir Lukman tun a satin da ya gabata wanda kuma har zuwa wannan lokacin basu shaki iskar yanci ba.
Yankin na Aseyori na yawan fama da farmakin 'yan bindiga inda ake yawan yin garkuwa da al'ummar kauyen. Hakan yasa mazauna garin Alagbado, Ogidi, Okolowo da wasu kauyuka suke ta guduwa suna barin kauyukan su saboda karuwar ayyukan 'yan bindiga.
Al'ummar wannan yankunan na fuskantar matsi daga wajen masu yin garkuwa da mutane. Lukman daya daga cikin wanda lamarin ya shafa wanda 'yan bindiga su 6 suka kawo hari gidansa suka yi awon gaba da ya'yansa 2 a ranar Laraba.
'Yan bindigan sun fara neman kudin fansa miliyan 20 wanda bayan doguwar tattaunawa har aka dawo miliyan 8 idan kuma bai kawo kudin ba sun yi barazanar kashe yaran nasa biyu.
SaharaReporters ta gano cewa Lukman ya sayar da motarsa kan kudi 1,500,000 sannan kuma yana neman wanda zai sayi gidansa domin ya samu ya kubutar da yaransa biyu.
Baya ga haka Lukman ya nemi 'yan uwa da danginsa da su taimaka masa wajen hada kudin domin kubutar da 'ya'yansa. Sannan ya yi rubutu a jikin gidansa inda yace yana bukatar a sayi gidansa cikin sauri.
No comments