Wace cuta ce ake kira Varicocele Varicocele wata cuta ce wacce take faruwa a cikin marainan mutum(Testicles) su yayan maraina akwai wata fa...
Wace cuta ce ake kira Varicocele
Varicocele wata cuta ce wacce take faruwa a cikin marainan mutum(Testicles) su yayan maraina akwai wata fata data rufe su wacce ake kira da (scrotum) a cikin wannan scrotum din akwai wasu jijiyoyin da suke samar da jini da kuma oxygen ga sauran sassan gaban da Namiji.
Wadan nan jijiyoyin suna kawo jini cikin reproductive gland sannan su mayar dashi zuwa Zuciyar mutum domin wajen ya kasance yana aiki a kowanne lokaci,samun wata matsala kamar kumburinko ciwo ga wadan nan jijiyoyin yana jawo wannan cuta da ake kira Varicocel.
Kai tsaye zamu iya cewa abinda ake cewa cutar varicocele shine kumburin jijiyoyin jini wadan da suke cikin fatar maraina wadan da suke rana jini tsakanin reproductive gland na da Namiji.
Sannan idan wannan matsala ta faru mutum zai samu nakasa wajen ruwan maniy din sa,wanda har hakan yana jawo rashin haihuwa idan wannan matsala ta samu mutum.
Sannan ita wannan cuta anfi samun ta ne lokacin balagar Namiji kuma tafi kama dan maraina na hannun hagu,amma tana iya kama duka marainan guda buyu wani lokacin.
Sannan kuma wani sa'in wannan cuta ta varicocele bata cika hana haihuwa ba kamar yadda masana suka bayyana,wani lokacin kuma tana hana haihuwa baki daya.
Mafi yawan lokaci idan kana da wannan cuta yana iya zama bbau wata alama da zaka ji,amma zaka iya gane cewa akwai sauyi a yayan marainan ka kamar;
1. Ganin wani kumburi a jikin daya daga cikin marainan naka.
2. Jin ciwo ko zafi daga cikin fatar maraina.
3. Gabin jijiyoyin da suke cikin fatar maraina sunyi girma sosau ta yadda zaka iya ganin su daga waje idan ka kalla.
4. Kankancewar maraina wanda cutar ta kama
5. Jin kaikai a fatar maraina
6. Rashin haihuwa
7. Chanjawar dan maraina.
Menene yake jawo wannan cuta ta varicocele.
Akwai wasu jijiyoyi da ake kira da spermatic cord wadan da sune suke rike da yayan maraina a tare dasu kuma akwai jijiyoyin na jini wadan da suke kai jini daga maraina zuwa fatar maraina wanda a jarshe jinin zai kuma zuciya ne.
Wani lokacin ana samu jinin baya komawa zuciyar yadda ya kamata hakan yake saka wadan jijiyoyi na jini su kumbura su haifar da wannan matsala ta Varicocele.
Masana suka ce babu wani abu da zaa iya cewa shine yake jefa mutum zuwa ga hatsarin kamuwa da wannan ciwo,kuma kai tsaye ace gaa abinda yake jawo shi baa sani ba.
A takaice abinda zaa samu a wannan bayani nawa na yanzu kenan.
Daga dan uwan ku Drmaijalalaini 08137482786
Allah yasa mu dace.
Daga Maijalalaini Islamic medicine 08137482786 WhatsApp 0r Call 08088863000 daga 12 na rana zuwa 10 na dare.
Muna jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist muna budewa 12 na rana zuwa 8 na dare.
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :
Copyright BY: maijalalaini Islamic chemist
FACEBOOK GROUP: maijalalaini Islamic chemist
EMAIL: drmaijalalaini
FACEBOOK PAGE LIKE: maijalalaini Islamic chemist
WhatsApp: 08137482786
Domin shiga group na Telegram 👇👇👇👇 https://t.me/joinchat/Q6DAL6WHKhhrxxZo
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati
Share.
No comments