Sabbin magunguna:

latest

Previous

Maganin furfura yadda zaa magance ta cikin sauki

 Maganin furfura yadda zaa magance ta cikin sauki (GREY HAIR)Kamar yadda muka sani gashi yana sauyawa suna zama sabbi sannan suna mutuwa sab...

 Maganin furfura yadda zaa magance ta cikin sauki




(GREY HAIR)Kamar yadda muka sani gashi yana sauyawa suna zama sabbi sannan suna mutuwa sabbi na zuwa,daga kuma lokacin da ka fara girma(tsufa) sai yanayin sauyawar sa ya zama kala daya ya zama ya dena sauyawa yadda ya kamata sai zuwa ruwan toka ko kuma fari.



Wannan farin shine ake cewa dashi furfura,wasu kuma na ganin cewa fitowar furfura alama ce ta girma da kuma nunin cewa mutum yana da hikima ne.



Duk da ana ganin furfura alama ce ta manyan ta wasu kum na kallon ta a matsayin baiwa ko kuma alamar hikima a tattare da wanda yake da ita.


Sannan takan zama alama ta karancin wasu sinadarin da jiki yake bukata wajen samar da lafiyayyen gashi wanda babu wata matsala a tare dashi.



Ga hanya da zaa bi domin a magance wannan yanayi.



Na farko



A samu man kwakwa a rika shafa a wajen da furfurar take a lokacin kwanciya zuwa safiya a wanke kai.



Na biyu



A samu albasa a markade ta a rika shafawa a kai bayan minti 15 a wanke da shampoo ko sabulu.



Na uku



A samu garin citta me kyau a hada da zuma a rika shan chokali daya a rana.



Wadan nan sune wasu daga hanyoyin da zaa bi insha Allah domin samun dacewa.



Sannan ayi kokari a rika amfani da abunuwa masu dauki na:-


B vitamins, Musamman B-12 and biotin

vitamin D

vitamin E

vitamin A

A rika kokari samun minerals Musamman wadan da suke taka muhimmiyar rawa bangaren gashi kamar su


zinc

iron

magnesium

selenium

copper


Allah yasa mu dace.


Daga Maijalalaini Islamic medicine 08137482786 WhatsApp 0r Call 08088863000 daga 12 na rana zuwa 10 na dare.

Muna jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist muna budewa 12 na rana zuwa 8 na dare.


SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :


Copyright BY: maijalalaini Islamic chemist 

FACEBOOK GROUP: maijalalaini Islamic chemist 

EMAIL: drmaijalalaini 

FACEBOOK PAGE LIKE: maijalalaini Islamic chemist 

WhatsApp: 08137482786 


Domin shiga group na Telegram 👉 Telegram



Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati


Share

No comments