Ku kasan zaka iya Daukar infection koda bakai jima'i ba. Abu me sauki ne ka dauki cutar da ake kira da Sexual Transmitted infection (St...
Ku kasan zaka iya Daukar infection koda bakai jima'i ba.
Abu me sauki ne ka dauki cutar da ake kira da Sexual Transmitted infection (Sti) ba tare da ka sadu da mai lalurar ba.
TAYAYA?
Da farko menene ake kira da Sexual Transmitted infection (Sti) sune infection da ake dauka a lokacin saduwa,saduwar zata iya zama saduwa farji da farji,ko saduwa ta dubura ko ta baki.
Akwai da yawa daga cikin wadan nan (Sti) wadan zaka iya dauka cikin sauki wasu ma ta hanyar yin Sunbata wato (kiss) zaka iya daukar su,wasu kuma baa dauka ta wajen yin kis.
Ga kadan daga cikin wadan nan Cututtuka na (Sti)
1. Hiv
2. Hepatitis B
3. Gonorrhea
4. Chlamydia
5. Genital herpes
6. Human papillomavirus
7. Syphilis
Wadan nan kadan daga ciki kenan.
Mu dauki guda 3 daga cikin wadan nan wadan da ake yawan samun su tsakanin maza da mata.
1. Chlamydia
2. Gonorrhea
3. Syphlis
Wadan nan suna daga cikin (Sti) da ake yawan samun mutane sun kamuwa dasu cikin sauki.
Kadan daga cikin hanyoyin da zaka iya kamuwa dasu.
1. Kiss (sumbata)
2. Yin jima'i ta baki (Oral sex)
3. Amfani da brush dame wannan cuta yayi amfani.
Sauran kuma kamar su
1. Hiv
2. Hepatitis B
Zaka iya koda bakai jima'i ba.
1. Ta hanyar zuba maka jinin mai dauke da ciwon.
2. Ko amfani da wuka ko reza wacce mai wannan cuta yayi amfani da ita taji masa ciwo.
Maana dai jinin ka idan ya hadu da me wannan ciwo shima zaka iya daukar wannan ciwo kai tsaye.
Sannan kamar
1. Genital herpes
2. Human papillomavirus
Ana daukar au kai tsaye da hanyar haduwa fata da me dauke da ciwon,ko amfani da wando riga zani tawul dame cutar yayi amfani dashi.
Allah ya tsare mu ya kare mu.
Zamu kawo bayani akan magani akan kowacce cuta daga wadan da muka lissafa insha Allah,da kuma alamomin kowannae.
Allah yasa mu dace.
Daga Maijalalaini Islamic medicine 08137482786 WhatsApp 0r Call 08088863000 daga 12 na rana zuwa 10 na dare.
Muna jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist muna budewa 12 na rana zuwa 8 na dare.
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :
Copyright BY: maijalalaini Islamic chemist
FACEBOOK GROUP: maijalalaini Islamic chemist
EMAIL: drmaijalalaini
FACEBOOK PAGE LIKE: maijalalaini Islamic chemist
WhatsApp: 08137482786
Domin shiga group na Telegram 👉Telegram
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati
Share.
No comments