CUTAR SYPHILIS ABINDA YAKE JAWO TA DA YADDA ZAKU KARE KANKU Menene syphilis? Syphilis wata cuta ce wadda za ta iya yaduwa ta hanyar jima...
CUTAR SYPHILIS ABINDA YAKE JAWO TA DA YADDA ZAKU KARE KANKU
Menene syphilis?
Syphilis wata cuta ce wadda za ta iya yaduwa ta hanyar jima'i,cutar syphilis na faruwa ne ta hanyar wani nau'in kwayar cuta da ake kira Treponema pallidum.
Mutane suna samun kamuwa da wannan cuta sannan su warje daga cutar syphilis tsawon É—aruruwan shekaru.
Syphilis na iya zama ƙalubale wajen gano shi a jikin mutum. Wani zai iya samun shi ba tare da nuna alamun cutar ba tsawon shekaru. Anfi samun waraka da farkon gano cutar kan ace cutar ta kwana 2 baai magani ba, wanda tana jawo cutar Ciwon huhu wanda idan aka bari baai magani ba zai shafi wasu sassa na jiki kamar Zuciya da kuma kwakwalwa.
Maganin sanyi kowanne iri cikin sauki fisabilillah
Fahimtar alamomi da abubuwan da ke haifar da syphilis na iya taimaka maka ka kare kanka. Idan kana da syphilis sannan ka gano kana dauke dashi zaka fi saukin samun waraka daga matsalar akan wanda baisan alamomin cutar baki daya ba.
Bari muga abubuwan da suke jawo wannan ciwo da kuma wadan da suke cikin hadarin kamuwa dashi .
Abubuwan da suke jawo cutar syphilis.
Cutar syphilis tana faruwa ne ta hanyar kamuwa kwayan cutar bacteril infection . A cikin 1905, masana kimiyya na Jamus sun gano cewa kwayar cutar Treponema pallidum ce ke da alhakin haifar da cutar.
Da farko, idan ka kamu da wannan ciwo yana iya zama babu wata alama da zaka iya gane cewa kana dauke da ita,kuma zata cigaba da zama a jikin ka tana haifar da matsaltsalu.
Maganin karfin maza saurin kawowa da kankancewar gaba
Ta yaya ake kamuwa da cutar syphilis?
Hanya guda daya tilo da ake yada cutar syphilis ita ce ta hanyar saduwa ta kai tsaye tare da wanda yaje dauke da ciwon syphilitic, ko hanyar wani ciwo wanda yake a ciki:-
baki
azzakari
farji
dubura
Cutar syphilis ana kamuwa da ita ta hanyar jima'i. Ma'ana za ka iya kamuwa da ita ta hanyar baka, dubura, ko ta farji, ko saduwa da al'aura kai tsaye.
Jarirai na iya kamuwa da syphilis idan mahaifiyar wacce dake dauke dasu tana da ciwon wanda kuma bata kula da magani. Ana kiran wannan da congenital syphilis,hakanan ana iya kamuwa da cutar syphilis ta hanyar ƙarin jini, ko da yake hakan yana da wuyar gaske.
Amma fa baa daukar wannan cuta a waja je kamat haka:-
* Amfani da bayan gida na kutane da yawa.
*Saka kayan da wani ya saka
*Amfani da abinci wanda mai cutar yaci
Wannan shi ne saboda kwayoyin cutar da ke haifar da syphilis basa iya rayuwa na mai tsawo a wajen jikin mutum.
Wanene ya fi fuskantar haÉ—arin syphilis?
Kowa na iya kamuwa da cutar syphilis. Koyaya, wasu dalilai na iya ƙara yuwuwar kamuwa da cuta. Ƙungiyoyin mutane masu zuwa suna da haɗarin kamuwa da syphilis:
Mutanen da suke jima'i ba tare da saka kwaroron roba ba na iya kamuwa da wannan cuta,wanda yake saduwa da mace fiye da daya sha yana cikin hadarin wannan cuta.
Matakan wannan cuta guda 4 ne kamar haka:-
primary
secondary
latent
tertiary
Maganin basir kowanne iri cikin sauki fisabilillah
Sannan kuma matakin cutar yana karuwa ne gwargwadon matakin da cutar take tana dadewa a jikin ka matakin ta yana karuwa.
Saboda haka da zarar ka fara jin daya daga cikin alamomin wannan cuta kayi kokari kaga likita.
Kadan daga alamomin wannan cuta;
1. Ciwon kai
2. Ciwon gabobi
3. Zazzabi
4. Zubewar gashi
5. Ramewa.
7. Rashin gani
8. Rashin ji
9. Rasa tunani
10. Matsalar kwakwalwa
11. Ciwon zuciya
Allah ya kiyaye mu ya kare mu
Maganin wannan cuta insha Allah yana nan zamu kawo shi bada jimawa ba.
Daga maijalalaini Islamic chemist kano 08137482786 08088863000.
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :
Copyright BY: maijalalaini Islamic chemist
FACEBOOK GROUP: maijalalaini Islamic chemist
EMAIL: drmaijalalaini
FACEBOOK PAGE LIKE: maijalalaini Islamic chemist
WhatsApp: 08137482786
Domin shiga group na Telegram 👇👇👇👇 https://t.me/joinchat/Q6DAL6WHKhhrxxZo
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati
Share.
No comments