Maganin Rashin haihuwa karin ruwan maniy maganin basir da maganin nakuda na mata insha Allah 1- Matar da ta dade bata samu haihuwa ba ta n...
Maganin Rashin haihuwa karin ruwan maniy maganin basir da maganin nakuda na mata insha Allah
1- Matar da ta dade bata samu haihuwa ba ta nemi Furen Albabunaj ta rika dafawa da ruwa kamar shayi, tana shansa tare da zuma. Kuma ta rika yin matsi da Man Albabunaj din ko Man Sazabu. Insha Allahu zata samu haihuwa.
2. Mutumin da yake da Qarancin ‘Ya’yan maniyyi. (Low Sperm Count) ya nemi Zaitul Lawus (Almond Oil) ya rika sanya cokali guda acikin ruwan shayi tare da zuma yana sha har tsawon sati uku. In sha Allahu ‘ya’yan maniyyinsa zasu yawaita, kuma zai samu haihuwa da izinin Allah.
3. Mutumin da Basur ya hanashi sakewa, ya yawaita cin tafarnuwa ko kuma hadiyar kwayoyinta. In sha Allahu zai samu sauki. Koda masu Ulcer (olsa) idan suka jarraba zasu dace. in sha Allahu.
4. Matar da take fama da matsalar Qarancin ruwan nono ta samu cokali bakwai na Hulba, Cokali bakwai na Yansun ta hada ta rika dafawa tana sha. in sha Allahu zata samu waraka, yaronta kuma zai girma cikin koshin lafiya.
5. Mace mai ciki, ta rika gauraya Garin habbatus Sauda da garin Zaitun cokali biyar biyar tare da garin kanumfari cokali daya. Ta zubasu acikin zuma mai yawa ta rika lasar cokali biyu safe da rana da yamma. in sha Allahu zata haihu lafiya, kuma jaririnta ma zai zama cikin koshin lafiya.
6. Idan mace tana nakuda, ana so a bata zuma ta rika sha. Daidai misali. In sha Allahu zata samu saukin zafin radadin nakuda.
7. Dattijai wadanda suka samu matsalar rikicewar Kwakwalwa da kuma Kananan yara idan ana so su samu basira mai karfi, arika dafa musu ganyen na’a na’a suna sha tare da Man hulba.
In sha Allahu kwakwalwarsu zata gyaru sosai. Kuma zasu rika haddace abu da wuri.
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :
Copyright BY: maijalalaini Islamic chemist
FACEBOOK GROUP: maijalalaini Islamic chemist
EMAIL: drmaijalalaini
FACEBOOK PAGE LIKE: maijalalaini Islamic chemist
WhatsApp: 08137482786
Domin shiga group na Telegram 👉TELEGRAM
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati
Share.
No comments