Me ka sani akan Cutar da ake kira hernia (kaba) Cutar Hernia wacce ake cewa gaba wani yanayi ne da yake samun mutum inda hanjin cikin mutum...
Me ka sani akan Cutar da ake kira hernia (kaba)
Cutar Hernia wacce ake cewa gaba wani yanayi ne da yake samun mutum inda hanjin cikin mutum yake bullawa ta hanyar tissue da tsokar jiki (bangon ciki),wanda wannan tissue din sune suke tare hanji ya tsaya a inda yake.
Kuma shi wannan wannan hernia yana fitowa ne yafi yawa a bangaren ciki da wajen mara ko saman da cibiya (Abdomen) sannan idan ya samu mutum baya tafiya da kansa sai anyi magani.
Kalolin wannan ciwo;
Hiatal hernia
Femoral hernia
Incisional hernia
Inguinal hernia
Abubuwan da suke jawo wannan cuta;
1. Shekaru
2. Tari wanda yayi Chronic
3. Ciwo wanda ya samu mutum Sanadiyyar wani aiki da akai masa aiki,ko mutum yaji ciwo.
4. Mace mai ciki
5. Yawan daukar abu mai Nauyi
Wadan da suke cikin hadarin kamuwa da wannan ciwo;
1. Mace mai ciki
2. Yawan shan taba
3. Tsufa
4. Masu matsalar bayan gida mai tauri,wanda yayi musu chronic
Alamomin gane wannan ciwo.
1. Ganin wani kulluto a ciki ko wani waje daga nan,amma idan ka tanna sai ya rika komawa.
2. Ganin wani kumburi a wajajen ciki ko kasan wajen mara.
3. Jin wani ciwo a wajen matsematsi ,wanda ciwon daga ciki ne.
4. Jin wani nauyi a matsematsi
5. Jin zafi ko wani ciwo a lokacin da mutum yake tari.
Don haka da zarar ka fara jin wasu alamomi daga ciki kayi kokari kaga likita.
Allah yasa mu dace.
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :
Copyright BY: maijalalaini Islamic chemist
FACEBOOK GROUP: maijalalaini Islamic chemist
EMAIL: drmaijalalaini
FACEBOOK PAGE LIKE: maijalalaini Islamic chemist
WhatsApp: 08137482786
Domin shiga group na 👉Telegram
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati
Share.
No comments