Abinda ya kamata masu yin mining na pi network su sani Har yanzu, darajar Pi Ï€ bai gama karÉ“uwa a kasuwar duniya ba, ma’ana, ba a iyankanc...
Abinda ya kamata masu yin mining na pi network su sani
Har yanzu, darajar Pi Ï€ bai gama karÉ“uwa a kasuwar duniya ba, ma’ana, ba a iyankance masa daraja ba. Su Dr. Chengdiao da Dr. Nicolas Kokkalis su gama arzikinsu, da engagements da traffic, ga ‘data’ na mutane da suka tara.
Pi π:
Ta iyu ya zama gaskiya, ya kai darajar da ake kirdado,
Ko ma ya wuce darajar da ake kirdado,
Ko ya gaza darajar da ake kirdado,
Ko ma ya yi failing (ba a fatan haka).
Ba wanda zai ce ma akwai tabbas, ba wanda zai ce ma babu tabbas, ana dai tsammani ne.
Amma dai burin da ake sa wa a kan Pi Ï€, ya wuce tunani, duk ‘pseudo-reality’ ne, ana jiran tsammani, har tsammanin na neman taÉ“a tunanin wasu mutane da yawa.
Ƙaddara darajar Pi Ï€ za ta zo a miliyoyin kuÉ—aÉ—e, ina da tabbacin, kaso 80% – 90%, nan da shekaru biyar za su Æ™ara faÉ—awa matsanancin talauci, me ya sa? A tunani da furuci, ‘liabilities’ mutane za su Æ™arawa kansu.
Akwai wata muƙala da Ayobami Sanusi (July, 2022) ya rubuta a shafin jaridar Tribune, kan dalilan da ya sa talaka ke dauwama a talauci guda 5:
Ba ya ƙoƙarin nema da kansa
Yana jiran wani ya zo ya ba shi
Ba ya tafiya da sauyin zamani
Bai san ya juya kuÉ—i ba, ko ka ba shi, kashewa zai yi
Ba ya duban wata dama ta samun kuÉ—i, sai dai ta kashe kuÉ—i
Percy Bysshe Shelley (1792 – 1822) ma ya faÉ—i makamanciyyar wannan a “A Defence of Poetry” (1840). Saboda a irin tunanin waÉ—annan, arziki shi ne kuÉ—i da kayan Æ™awa (luxuries).
Idan ka sami matalauta kamar mutum 100, ka raba musu Naira miliyan biyar-biyar (₦5m), bayan shekara biyar, da wuya ka sami kaso 10% daga cikin 100% nan da za su yi amfani da kuÉ—in wajen juyawa, su ci gaba. Sauran 90% É—in, sun sa yi gida, abin hawa, sutura, latest devices… sun dai kashe kuÉ—in, sun huce haushi da luxuries. Misali, a binciki waÉ—anda suka sami lamunin NISAL: 500K, 750k, 1m… shi ya sa Sunday Adelaja (2017) ke cewa: “Talaucin gaskiya, a tunani yake, ba a aljihu ba.”
Wannan jajircewar, da imani da ghaibu ga Pi Ï€, shi ne irin ‘ijtihadin’ da ake son mutum ya yi a duk wani lamari na rayuwarsa domin ya kai ga nasara. Da a ce a wani kasuwanci na dahir aka sa wa irin wannan ‘effort’ É—in, tabbas tsawon kwanakin da aka fara Pi Ï€, da labari ya sha-bamban.
No comments