Sabbin magunguna:

latest

Previous

Rashin haihuwa rashin kwayoyin maniy abubuwan sa suke jawo wannan cuta (Azoospermia)

 BAYANI AKAN ABUBUWAN DAKE HANA SAMUWAR KWAYOYIN MANIYY. Zamu fara da rashin haihuwa,idan aka ce rashin haihuwa ana nufin an samu kusan shek...

 BAYANI AKAN ABUBUWAN DAKE HANA SAMUWAR KWAYOYIN MANIYY.




Zamu fara da rashin haihuwa,idan aka ce rashin haihuwa ana nufin an samu kusan shekara daya da aure kuma ana saduwa ba yare da kariya ba(kwaroron roba) amma baa samu haihuwa ba,wannan shine wanda zai dauki kansa a matsayin wanda yake da lalura ta rashin haihuwa.


Akwai abubuwa da dama da suke jawo rashin haihuwa kama daga cuta da kuma kaddara ta Allah,akwai wadan da lafiyar su kalau amma cikin hukuncin Allah basu samu rabo na haihuwa ba.


Amma abinda za muyi bayani akan sa yau shine matsalar data shafi maza ta rashin kwayoyin maniyy baki daya(azoospermia).


Akwai matsala ta low sperm count (rashin karfin maniyy)wanda hakan yana hana haihuwa amma shi wannan lalura ta azoospermia kwatakwata baa samun kwayoyin haihuwa a cikin maniyy din da yake fita.


SHIN MENENE YAKE JAWO WANNAN CUTA TA (AZOOSPERMIA)


Masana a fannin lafiya sun bada sababai guda uku wadan da sune ke iya jawo wannan lalura ga d'a Namiji.


1. Pre-testicular azoospermia (yana daga cikin wadan da bada hana haihuwa)karancin hormones wanda yake da alhakin samar da maniy

2. Rashin lafiya ta diyan maraina (Testicles)(yana daga cikin wadan da basa yana haihuwa) ya zama yana da ciwo ko wata lalura.

3. Post-testicular azoospermia(yana hana haihuwa)matsalar toshewar wata hanya daga cikin hanyoyin haihuwa na da Namiji.


Kowanne a cikin wadan nan da muka lissafa yana da tashi gudunmawa da yaje badawa wajen rasa kwayoyin haihuwa baki daya.


BARI MUYI BAYANIN KOWANNE DAYA DAGA CIKIN WADANAN SABABAI 


1. Pre-testicular azoospermia



 Yana samuwa ne Sanadiyyar rashin daidaituwar kwayoyin halitattar mutum(genetic disorder) da kuma samun matsala a kwakwalwa musamman bangaren hypothalamus or pituitary gland( wannan sune manyan hormones na jikin mutum domin sune suke bada izini ga sauran hormones su gudanar da ayyukan su,sannan shan wasu kwayoyi ko a yiwa mutum aikin cancer shima yana jawowa.


2. Testicular azoospermia


Yana faruwa Sanadiyyar rashin yayan maraina a jikin mutum.


Ko rashin saukowar su gurbin su.


Ko wadan da akwai su amma basa samar da maniy baki daya.


Ko wadan da suna samar da maniy amma ba lafiyayye ba.



3. Post-testicular azoospermia


Wannan yana faruwa Sanadiyyar katsewar hanyoyin da suke fito da maniyy daga yayan maraina,kamar abinda ake kira da epididymis or vas deferens tubes.


vas deferens tubes shine bututun dake dauko maniy daga cikin yayan maraina zuwa epididymis idan aka rasa shi sandiyyar cutar da ake kira congenital bilateral(CBAVD)


ALAMOMIN CUTAR AZOOSPERMIA


1. Karancin shaawa ko daukewar ta.

2. Saurin kawowa yayin jimai

3. Jin zafi ko walwalar yayan maraina.

4. Karancin gashi dake fitowa a fuska.


A takaice yan uwa wannan shine bayani akan wannan cuta ta rashin kwayoyin maniyy AZOOSPERMIA da zamu iya. kawowa.


Daga dan uwan ku drmaijalalaini 08137482786


Domin karin bayani ko bukatar magani hadadde muna jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist


Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati.


SHARE .





No comments