MAGANIN CIWON KUNNE KOWANNE IRI INSHA ALLAH Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu,yan uwa barkan mu da safiya da fatan mun wayi ga...
MAGANIN CIWON KUNNE KOWANNE IRI INSHA ALLAH
Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu,yan uwa barkan mu da safiya da fatan mun wayi gari cikin koshin lafiya,Allah ya kara mana lafiya.
Kamar yadda jiya mukai bayani game da maganin ciwon hakuri wasu sun bukaci na ciwon kunne,wanda dama kusan abu daya ne yake haddasa su wato "sanyi".
Shi yasa babu lokacin da suka fi matsawa mutum sai lokacin sanyi ko damuna,amma idan kasan kana yawan yin ciwon konne ko hakuri ko ciwon ido,to ka rika taammali da maganin sanyi, insha Allah zaka ga abun yana rabuwa dakai.
Game da maganin ciwon kunnen abun da zaka nema sune kamar haka.
ZA'A NEMI
1. Man zaitun
2. Man Tafarnuwa
YADDA ZAA HADA
Da farko zaka samu auduga ka goge kunnen naka sosai,sai ka hada chokali 2 na man tafarnuwa da chokali 1 na man zaitun,zaa rika diga digo uku a konnen da yake ciwo ko kaikayi ko yawan kuka da dare kafin kwanciya,asa auduga a toshe zuwa safiya a cire a sake goge kunnen.
Haka za'ai har a samu waraka.
Domin karin bayani ko neman maganin mu hadadde sai a kira mu a 08137482786 ko a OFFICE namu dake cikin jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @ maijalalaini islmic chamest.
Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati.
LIKE AND SHARE.
No comments