Sabbin magunguna:

latest

Previous

CUTAR POSTPARTUM CARDIOMYOPATHY (PPCMP) (Ciwon zuciyan bayan Haihuwa)

CUTAR POSTPARTUM CARDIOMYOPATHY (PPCMP) (Ciwon zuciyan bayan Haihuwa) Mata iyayen Al'ummah ! Duk wanda ka gani a raye to uwa ce ta haife...

CUTAR POSTPARTUM CARDIOMYOPATHY (PPCMP) (Ciwon zuciyan bayan Haihuwa)





Mata iyayen Al'ummah ! Duk wanda ka gani a raye to uwa ce ta haife shi. Kafin haihuwa iyaye mata su na haduwa da jarrabawa Iri-Iri a lokacin da su ke dauke da juna biyu, soboda canje-canjen da jikinsu ya ke yi. 


Daga cikin matsalolin da ya ke takurawa mata masu juna biyu, musanman lokacin da cikin ya ke wata tara da wata biyar bayan haihuwa, akwai Ciwon Zuciya wanda ake kiranshi da Postpartum Cardiomyopathy. 


Zuciya wata curarriyar nama ce mai kwaroron jijiyoyi guda hudu Wanda jini ya ke shiga ya fita da ga Zuciya. Amfanin Zuciya Suna da yawa amman mafi muhimmanci shi ne Karbar jinin da babu Oxygen daga jiki , Tura shi zuwa Huhu don daukan Oxygen, sai Tura Jinin mai Oxygen zuwa Jiki. 


In Zuciya ta samu matsala, ba za ta yi aikin ta yanda ya kamata ba. Jinin sai ya taru a cikin ta da jijiyoyin da su ke kaiwa da dauko jini daga Huhu, haka ma jijiyoyin da su ke dawo da jini daga jiki za su cika da jini. Yawan jinin a cikin jijiyoyin ya ke kai ga taruwan ruwa a Huhu da kuma Hanta wani lokaci har Koda yake tabawa. 


Kusan haka ya ke faruwa ga Mata Masu Ciwon PPCMP. Ana su bangaren Muscle din Zuciya ne waton Myocardium su ke kumbura, sai ya sa zuciyar ta girma sosai har ya kai wasu cells na zuciyar su fara mutuwa. Daga karshe ya haifar da Ciwon Zuciya... Wanda bai da takamemmen dalili guda da ya kawo shi, sai dai abubuwan da ake hasashen su na kawo shi. Wasu matan masu wannan ciwon basu da wata ciwon da zai iya kaiga ciwon zuciyan kafin daukan cikin. 


Ciwon na warkewa gaba daya komai tsananin shi, saboda ya na da magani, in an je asibiti akan lokaci, wasu kuma daga nan Sun kamu da ciwon zuciya kenan. Wasu kuma shi yake ajalinsu musanman in ba a je asibiti da wuri ba. Allah ya kiyaye. Amin.


Mata masu juna biyu Da aka fi samun su da wannan Ciwon, da kuma abubuwan dake kara tsananin ciwon sun hada da:


👉 Wadan da su ka fi shekaru talatin..

👉 Wadan da Su ka sa mu lalurar rashin jini lokacin da suke da ciki.

👉 Ma su Ciwon Asthma.

👉 Mai Cikin yan biyu.

👉 Ma su hawan jini.

👉 Ma su shan taba..

👉 Ma su shan giya..

👉 Rashin Ingantaccen abinci..

👉 Kiba da rashin Motsa jiki.

👉 Genetic... Gado ta hanyar kwayan halitta.

👉 Autoimmune disease dss.


Alamomin ciwon sun hada da:


▶ Yawan Gajiya da Rashin Karfin Jiki.

▶ Numfashi Sama sama, ko da a kwance. Yakan karo a likacin tafiya ko yin wani aiki.

▶ kumburi A Kafa, Hannu harda Ciki.

▶ Bugawan Zuciya da karfi..

▶ Tari.

▶ Kumburin jijiyoyin wuya... Dss


Wasu daga cikin alamomin normal ne a Watan karshe na haihuwa. Amman ya na da kyau a je aga likita da wuri don neman shawaran masana da yin gwajegwaje..


In mace na da wannan matsalar yana da kyau ta rage shan gishiri, rage shan ruwa kadan, ta dinga duba nauyinta akai akai, sa'annan ga mai shan taba da giya duk su daina. 


Ya na da kyau a je awun ciki akan lokaci musanman masu matsalar rashin lafiya na ko wace iri ne. 


Ma'aikatan kananan asibiti ba nakasu bane ki/kayi referring din mai ciki da ki/ka ga tana da matsalar da ta fi karfinki/ka tun wuri kafin abun yayi tsanani.. Ke kuma ba mugunta bane in anyi referring din ki asibiti na gaba.


Mu kula da lafiyar Iyayen mu mata. Allah ya karawa mata masu dauke da juna biyu juriya da Lafiya. Ameen Ameen Ya Allah 


MU KWANA LAFIYA.


Almustapha Muhammad Gama.


SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :


Copyright BY: maijalalaini Islamic chemist 

FACEBOOK GROUP: maijalalaini Islamic chemist 

EMAIL: drmaijalalaini 

FACEBOOK PAGE LIKE: maijalalaini Islamic chemist 

WhatsApp: 08137482786 



Domin shiga group na Telegram 👇👇👇👇 https://t.me/joinchat/Q6DAL6WHKhhrxxZo



Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati


Share.



No comments