Bayani akan cutar Pelvic inflammatory disease wato(Pid) Ciwon kumburin mahaifa shine kumburin gabobi na mace kamar mahaifa, ovaries, cervix...
Bayani akan cutar Pelvic inflammatory disease wato(Pid)
Ciwon kumburin mahaifa shine kumburin gabobi na mace kamar mahaifa, ovaries, cervix, endometrium, da madaukan mahaifa wato fallopian tube, saboda kamuwa da kwayoyin cutar da ake dauka ta hanyar jima'i. Wani lokaci kuma yana haifar da ƙwayoyin cuta na al'ada da ke cikin farji. Wannan kwayar cutar tana shiga ta cikin farji kuma ta kai harga mahaifa, fallopian tube, da ovaries. Idan ba'a kula da PID na dogon lokaci ba, to zai iya haifar da matsaloli masu hatsari.
ABUBUWAN DA SUKE JAWO PID
1. Tushen abubuwan da ke haifar da PID galibi daga Cututtukn da ake É—auka ta hanyar jima'i ne kamar gonorrhea da chlamydia.
2. Hakanan ana iya yada ta daga cututtukan da ba a É—auka ta hanyar jima'i kamar su bakteriya vaginosis.
3. A wasu lokuta cututtukan hanji masu fashewa na iya haifar da PID.
4. Jima'i mara tsaro na iya haifar da PID cikin sauƙi.
5. Samun tarihin baya na PID da STD.
WADAN DA SUKE CIKIN HADARIN KAMUWA DA WANNAN CUTA
1. Mace mai shayarwa
2. Mace wacce tayi bari
3. Macen da take da abokan tarayya da yawa(neman maza)
4. Mace mai shekaru kasa da 25 kuma ake saduwa da ita.
ALAMOMIN KAMUWA SA WANNAN CUTA TA PID
1. Yawan ciwon ciki
2. Warin gaba
3. Zafi lokacin jima'i
4. Yawan jin zazzabi ko sanyi
5. Yawan yin fitsari
6. Yawan amai.
HANYOYIN KARIYA DAGA CUTAR PID.
1. Gwajin cutar kafin ayi jimai(gwaji kafin Aure)
2. Yawan gwajin cutar akai akai
3. Saka kwaroron roba wajen jima'i
4. Rage abokan yin jima'i.
5. Tsaftar gaba a kowanne lokaci.
Allah yasa mu dace
Daga maijalalaini Islamic chemist 08137482786 muna jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist.
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :
Copyright BY: maijalalaini Islamic chemist
FACEBOOK GROUP: maijalalaini Islamic chemist
EMAIL: drmaijalalaini
FACEBOOK PAGE LIKE: maijalalaini Islamic chemist
WhatsApp: 08137482786
Domin shiga group na Telegram 👇
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati
Share.
No comments