AMFANIN KANINFARI GUDA TAKWAS(8)A JIKIN DAN ADAM DA YADDA AKE AMFANI DASHI IDAN KA KARANTA KA TURA ZUWA GA SAURAN YAN UWA DOKIN SUMA SI AMF...
AMFANIN KANINFARI GUDA TAKWAS(8)A JIKIN DAN ADAM DA YADDA AKE AMFANI DASHI
IDAN KA KARANTA KA TURA ZUWA GA SAURAN YAN UWA DOKIN SUMA SI AMFANA
Kanumfari nada Amfani ga lafiyar dan Adam domin yana Maganin Fungal, Bacteria da Virus cututukkan da bama iya ganin su kai tsaye ba tare da an saka madibin Likita ba (micro scpt).
A kasashe da dama ana amfani da kanumfari, kamar su Indunisia, America, India da Sauran kasashen turai, Yankin Africa ma ba'a bar mu a baya ba domin kusan ma duk mun fi sauran kasashe amfani da Kanumfari in ka debe India
domin gaba daya kasar India ba inda ba'a amfani da Kanumfari Musamman ma bangaren yankin Arewa na India.
America Sukanyi amfani da kanumfari wajen girki da kuma saka shi a Buredi.
A kasar Netherland sukanyi amfani da shi wajen hada wainar Fulawa (cheese).
A kasashen Chana da Japan sukan yi sabulun da Kanumfari domin magance cutukkan da ke addabar fata.
YADDA ZA'A YI AMFANI DA KANUMFARI WAJEN NEMAN LAFIYA
1.CIWON KAI
(A), Yana maganin ciwon kai. A shafa
man kanimfari a goshi, Yana taimakawa
wajen ciwon kai wanda ke faruwa sanadiyar mura.
(B), Idan kuma ciwon kan bana Mura bane, za'a iya samun Kanumfari guda biyar a saka a cikin ruwa kofi guda, a saka a wuta su tafasa sosai sai a saka Suger kamar Rabin cokali a ciki idan
ya dan huce sai a sha ayi haka sau 2 a yini In shaa Allahu kan zai daina ciwo koda kuwa baya jin Magani ne.
2. CIWON HAKORI
Yana maganin ciwon hakori. Zaka
iya amfani da man-kanimfari (clove oil)
ga hakori mai-ciwo ko kuma kanimfarin
(dakakke) , a jikashi kadan da ruwa a
lika wajen hakori mai-ciwo. Idan mai
( clove oil) kake amfani dashi sai asamu auduga a zuba man kadan a lika wajen hakori mai-ciwo (ka danne da hakora).
3.WARIN BAKI
Za’a iya amfani dashi a matsayin abun wanke baki. Yana maganin warin baki (a tafashi a yawaita wanke baki dashi sau 3 a rana).
4.MAGANIN AMAI
(A), Domin Tsayawar amai ga Mata masu ciki, a daka kanunfari biyu a sa babban cokali daya na zuma a sha yana maganin Amai ga macce mai ciki.
(B),Don magance amai baga mai juna biyu ba kuwa, a saka kanumfari 4 a cikin ruwa kofi daya a tafasa idan ya tafasa a saka sugar cokali daya a sha.
5.TYPHOID
A samu ruwa littr biyu sai a saka kanumfari kamar guda 5 a cikin ruwan a tafasa ruwan kada a sauke sai ruwan sun koma sauran littr daya sai a sauke idan suka huce sai a riqa sha Wannan yana Maganin typhoid.
6. Ciwon Kunne;
A hada Man kanun fari da Man Ridi diga a kunne mai ciwo duk lokacin da za'a kwanta wannan yana maganin ciwon kunne.
7.MAGANIN MURA
Ga masu su mura A tafasashi da citta/jinja (ginger) a sha shayi.
8. MAGANCE MAKERO/KYANDA
Ana goga Man kanumfari a wurin da matsalar tace wannan yana maganin Makero.
ALLAH YASA MU DACE
Domin shiga group namu
👇
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama salati
LIKE AND SHARE ➡️
No comments