Amfanin Goruba masu matukar amfani ga lafiya. Idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana 🙏. GOROBA wata bishiya ce da ta da...
Amfanin Goruba masu matukar amfani ga lafiya.
Idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana 🙏.
GOROBA wata bishiya ce da ta dade a duniya sannan an fi samun ta ne a kasashen Afrika. Bincike da aka gudanar akan goruba ya bayyana mamora da kuma alfanu da dama da take da shi, sakamakon sunadaran flavonoids, saponins da tananis, wanda wannan sunadaran ba sabon abu ne a wurin masana kiwon lafiya da likitoci.
Baya ga fa’idar ta wajen magance cututtuka ana amfani da ganyan ta wajen yin igiya, Kwando da tabarma.
Wannan ya sa muka binciko maku maganin cututtuka da Gorub ke yi a jikin dan adam. Amfanin Goruba 10 ga lafiyar jikin dan Adam Ga su kamar haka:
1. Masu fama da cutar asma za su iya shan garin kwallon goruba a cikin tafashashen ruwa.
2. Yana taimakawa masu samun matsala lokacin fitsari.
3. Shan garinta a ruwan dumi na taimakawa masu karancin jini a ji.
4. Goruba na maganin matsalar hawan jini.
5. Haka zalika goruba na magance cutar basir. 6. Yana kuma kare mutum daga kamuwa da cutar daji.
7. Cin goruba na kara karfin namiji.
8. Yana kuma rage kiba a jiki.
9. Cin goruba na kara karfin kashi da hakora. 10. Ruwan jikakkiyar goruba na tsiro da gashin mutum idan dai aka wanke kai da shi.
Ana daga garin ta kamar shayi ana sha sau biyu a rana,ga dadi ga magani idan kuma zaka iya ana ci haka kawai.
Daga shafin maijalalaini Islamic chamest.
Domin shiga group na Telegram 👇👇👇👇 https://t.me/joinchat/Q6DAL6WHKhhrxxZo
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati.
Share🙏
No comments