KO KU NA DA BuKATAR KU SAN ABUBUWA 10 DA MADACIYA TA KUNSA? TO KU DAURE KU KARANTA; 1. Jakar maÉ—aciya dai wata jaka ce da Allah ya ajiyeta a...
KO KU NA DA BuKATAR KU SAN ABUBUWA 10 DA MADACIYA TA KUNSA? TO KU DAURE KU KARANTA;
1. Jakar maɗaciya dai wata jaka ce da Allah ya ajiyeta a cikin ciki kuma ta na nan ɗamfare da hanta daga ƙasan hantar a ɓangaren dama daga sama a cikin ciki.
2. Hanta ce ke samar da ruwan maɗaciya wanda ke da launin kore ko kuma rawayar gwal, sannan ruwan maɗaciyar ya gangaro zuwa cikin jakar maɗaciya domin ajiya zuwa lokacin da za a buƙace shi domin sarrafawa da kuma rarrabewa tsakanin duk wani abu bako da ya shigo cikin ciki.
3. Hanta na iya samar da ruwan maÉ—aciya da yawansa ya kai 800 – 1200 mL a kullum. A yayin da jakar maÉ—aciyar ke iya cin ruwan maÉ—aciyar da yawansa ya kai 50 mL bayan ta tace mafi yawan ruwan da ke ciki.
4. Ruwan maɗaciya ya ƙunshi kaso 97.6% ruwa zalla da kuma kaso 2.4% na gishirin maɗaciya da sauran ɓurɓishin ma'adanai da sauransu.
5. Gishirin maÉ—aciya shi ne jigon aikin maÉ—aciya a jikin É—an Adam musamman wajen narka abinci.
6. Gishirin maɗaciya shi ne jigon sinadarin da ke narka ko markaɗa abinci ajin mai ko kitse a cikin ƙaramin hanji har a mayar da shi zuwa yadda jiki zai iya zuƙe shi daga ƙaramin hanji zuwa sassan jiki.
7. Gishirin maɗaciya na taimakawa wajen yi wa hanta ƙaimi domin samar da ruwan maɗaciya.
8. Har'ila yau, gishirin maɗaciya na taimakawa wajen sauƙaƙa fitowar bayan-gida (kashi) daga cikin babban hanji zuwa dubura. Kuma daga cikin ruwan maɗaciya ne bayan-gida ke samo launin ruwan ƙasa da yake da shi.
9. Tsakuwar maÉ—aciya: A yayin da kwalastirol ya hauhawa a jiki, kwalastirol na iya curewa ya haifar da matsalar da ake cewa tsakuwar maÉ—aciya wato "gallstone" a turance. Gishirin maÉ—aciya na taimakawa wajen magance curewar kwalastirol a cikin jakar maÉ—aciya.
10. Duk da É—imbun alfanun maÉ—aciya ga jikin É—an Adam, a na iya tiyatar cire jakar maÉ—aciyar idan a ka samu matsalar tsakuwar maÉ—aciya kuma magunguna su ka gaza magance tsakuwar.
Ya Allah ka kara mana lafiya.
No comments