Yadda mace zata zama mai Niima a koda yaushe. sami ayarki ki tsinceta tas sannan ki wanke ki shanya, idan ta bushe sai ki zuba a turmi ki da...
Yadda mace zata zama mai Niima a koda yaushe.
sami ayarki ki tsinceta tas sannan ki wanke ki shanya, idan ta bushe sai
ki zuba a turmi ki dakata lukwi, ki na dakawa kina tankadewa da rariya mai
laushi, sanya amarya kuka sai ki daka dabinonki da cukwi da mazar kwaila da
hakin daka lukwi ki hada da dakakkiyar ayarki guri guda, ki sami mazubi na
roba mai kyau mai murfi ki zuba, duk sanda zaki dinga sha sai kisa madara
peak ko kuma fresh milk danyen nono ko yoghurt me kyau, ba a bawa yaro
mai kiwa.
*▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒*
*_■ HADIN NI'IMA 2 ■_*
❍ aya
❍ dabino
❍ tafarnuwa
❍ sugar da madara
YADDA AKEYI
zaki sami ayarki ki jika ta ta jiku sannan ki surfata, ki jika dabinon ki shi ma
ya jiku sosai sai a markada da dan blander ko kuma a markado a inji amman kice sai an gama nikan gero sannan za'a nika miki don kada a nika a kan kayan miya don kada yayi yaji, sai ki zuba garin tafarnuwa a kai sai ki hada
da madara ko nono idan da hali a saka a firji yayi sanyi ko kuma a sanya kankara a kai a sha ba a bawa yaro.
_▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒_
*_✰ HADIN NI'IMA 3 ✰_*
_gwanda_
_kankana_
_abarba_
_lemon zaki_
_kankara_
_sugar_
YANDA AKEYI
zaki sami gwandarki da kankanarki da abarba da ayaba ki yayyanka gwitsi
-gwitsi kamar kan kuda ' inji yara- sai ki bare bayan lemon zaki ki shima har
da wannan farar fatar ki cire kwallayen suma sauran ki ciccire kwallayen sai ki
hada su guri daya ki kara ruwan kadan kisa sukari kadan idan kina da firji kisa
a ciki idan kuma babu ki sak kankara akai ki ajiye shi narke sai ki tsiyaya
ruwan zaki ga ya zama mai kauri kitib ki dinga sha zaki iya hadawa da
yangudaddajin ma.
*▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒*
*✿・ HADIN NI'IMA 4・✿*
*dabino*
*madarar shanu*
*kanunfari gari*
*kirfa*
YADDA AKEYI
za'a sami dabino a shanya shi ya bushe sai a cire kwallon a dakashi lukwi,
sannan a saka dakakkan garin janunfari a hada a kurfa guri daya sai a dinga
zuba cokali uku ana hadawa da madara shanu ana sha safe da yamma cokali
uku uku kullum tsahon sato guda.
▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒
Maijalalaini Islamic chemist kano 08137482786
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati.
Share.
No comments