Sabbin magunguna:

latest

Previous

Kwanciyar Azzakari a daidai lokacin saduwa abinda yake jawo da kuma magani

 Kwanciyar Azzakari a daidai lokacin saduwa abinda yake jawo da kuma magani Da yawa yan uwa suna korafin cewa sai sunzo kusantar iyalin su s...

 Kwanciyar Azzakari a daidai lokacin saduwa abinda yake jawo da kuma magani


Da yawa yan uwa suna korafin cewa sai sunzo kusantar iyalin su sai gaban ya kwanta ya zama karami koma bazai sake Tashi ba sai an fasa yin jima'i a lokacin.


Zaka ga indai wasanni zaai koda awa daya zaai gaban bazai kwanta ba,amma da zarar zaa shaga sai ya koma,ayi ayi yaki mikewa.


 Wani ma zai dena jin shaawar matar sa,amma idan yaga wasu matan a waje zaiji yana shaawar su duk wannan matsala ce ta Namijin dare wasu zaka ji suna cewa shima sanyi ne wasu amosanin mara wasu ma suce maka basir.


Amma akwai wasu abubuwa da suke kama da wannan amma suna da banbanci,kamar ciwon suga ko hawan jini ko damuwa ko wata matsala a tsakanin ma'aurata.


Amma banbanci shine koda waje kaje duk matsalar haka dai zaka ganta baza ta sauya ba,amma shi na jinnul Ashiq iya iyalin naka ne matsalar zata rika faruwa.


 Amma ga magani wanda insha Allah zaa rabu da wannan Matsala a samu waraka baki daya,amma idan iyalin ka tana fama da mafarkai ayi kokari itama ayi mata magani domin waraka baki daya.


 ABINDA YAKE NEMA SHINE.


 1. Furen tumfafiya

 2. Kan barawo barawo.


Furen tumfafiya shine farin abu wanda yake fitowa a karshen ganyen tumfafiya din,shi kuma kan barawa wani abu ne ball ball haka yana da kayoyi a jiki duk amma ana samu wajen yan ganye(masu maganin gargajiya)

 

Zaa samu su a shanya su bushe sai a dake su waje daya a rika turare dashi a gaba safe da dare insha Allah zaka samu rabuwa da wannan matsala baki daya.

 Zaai haka har tsawon sati biyu koda matsalar ta tafi zaa cigaba dayi ne har lokacin.


 Allah yasa mu dace.



 SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :


Copyright BY: maijalalaini Islamic chemist 

FACEBOOK GROUP: maijalalaini Islamic chemist 

EMAIL: drmaijalalaini 

FACEBOOK PAGE LIKE: maijalalaini Islamic chemist 

WhatsApp: 08137482786 

Domin shiga group na Telegram 👇👇 

TELEGRAM


Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati


Share.

No comments