Sabbin magunguna:

latest

Previous

SAURIN KWANCIYAR AZZAKARI DA RASHIN MIKEWAR SA.

Saurin kwanciyar Azzakari a lokacin jima'i  Yan uwa maza da yawa suna fama da matsalar rashin mikewar Azzakari ya tsaya yayi karfi wanda...

Saurin kwanciyar Azzakari a lokacin jima'i 





Yan uwa maza da yawa suna fama da matsalar rashin mikewar Azzakari ya tsaya yayi karfi wanda ake kira (Erectile dysfunction) wacce ake kira (ED) wannan cuta ta zama ruwan dare a rayuwar mazaje.

Kuma wannan matsala tana da wuyar shaani kasancewar ba lalura daya ke haifar da ita ba,cutuka da yawa sukan jawo wannan lalaura.

Hakan yana faruwa Sanadiyyar rashin shigar isashshen jini cikin jijiyoyin Azzkari wadan da sune ke saka shi mikewa ya tsaya yayi kwari da kuma karfi.

MENENE KE JAWO WANNAN CUTA

Kamar yadda muka fada a baya cutuka da yawa suna iya jawo wannan lalaura amma ga kadan daga cikin su.

1. Ciwon zuciya:Lallai wadan da suke fama da lalurar zuciya suna fama da wannan matsalar ta Ed sakamakon zuciya ita ce harba jini zuwa kowannne sassa na jikin dan Adam,da zarar ta samu rauni to hakan zai saka baza ta iya harba jini yadda ya kamata a kowanne sassa ba,hakan zai jawo jini bazai shiga mazakuta yadda ake so ba.

2. Prostate cancer (cutar kansa ta futustota) wannan wata cuta ce da take tsirowa a cikin prostate na maza,hakan yana jawo matsalar rashin mikewar Azzakari a lokacin shaawa.

Sannan wanda aka yiwa aikin wannan Cancer shima matsakar tana samun sa,saboda yanke jijiyo da ake a lokacin aikin.
3. Prostate enlargement wannan itama cuta ce wacce take haifar da kumburi a futustota ta da Namiji wanda hakan yake tushe hatta hanyar da fitsari ke fita,sakamakon hakan Azzakari bazai rika mikewa yadda ake so ba.

Sannan shan magunguna na wannan matsala suna jawo rauni ga Azzakari.
SAURAN MATSALOLIN SUN HADAR DA

1. Yawan kiba
2. Ciwon suga
3. Yawan kitse
4. Ciwon koda
5. Karancin hormones (testosterone)

MATSALOLIN DA SUKE JAWO WANNAN CUTA WADAN DA BA LALURA BA.

1. yawan damuwa
2. Yawan tunani
3. Bacin rai
4. Matsala a tsakanin maaura ta

Da sauran su

A takaice wadan nan sune masu matsaloli dake jawo matsalar raunin Azzakari da ake kira da (Erectile dysfunction).

Daga zauren maijalalaini.com

Allah yasa mu dace

Domin magani ko karin bayani zaku iya tuntubar mu a 08137482786 ko office naku dake jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist

Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati.

SHARE



2 comments

  1. Minene maganin wanan matsalar mafi sauki.don Allah.?

    ReplyDelete
  2. Dan allah ka fada mana maganin wallahi nima yana damuna sako daga Abdul T ara

    ReplyDelete