Sabbin magunguna:

latest

Previous

Ko kasan me ake kira da cutar sanyin mafitsara Urinary tract infection

Urinary tract infection sanyin mafitsara  Cutar urinary tract infection (UTI) cutar mafitsara, cuta ce daga Æ™wayoyin cuta. WaÉ—annan Æ™ananan...

Urinary tract infection sanyin mafitsara 

Cutar urinary tract infection (UTI) cutar mafitsara, cuta ce daga ƙwayoyin cuta. Waɗannan ƙananan halittu ne da ba za a iya ganin su ba tare da naurar microscope ba. Yawancin UTIs ƙwayoyin cuta na bacteria sune ke haifar da su, amma wasu suna samuwa ne daga fungus ( fungi) cutar mafitsara (UTI) suna cikin cututtukan da suka fi yawa a cikin mutane.


 UTI na iya faruwa a ko'ina a cikin hanyoyin mafitsara,wanda ya hadar da kidney(koda) ureters (hanyar fitsari daya sauko daga koda) bladder (inda fitsari ke taruwa a jiki) da kuka urethra (hanyar da fitsari ke fita daga jiki) wannan nan sune ake kira Urinary tract.


Cutar mafitsara ta (UTI)ta kasu gida biyu akwai mafi sauki da karancin hadarin kamuwa da ita wacce ake kira da lower track,shine infection wanda yake cikin iya waje biyu, na farko urethra (hanyar da fitsari ke fita daga ciki,da kuma bladder (inda fitsari ke taruwa wannan shine ake kira da lower track.


Sannan akwai wanda ake kira ta Upper track,shi wannan yafi hadari domin yana faruwa ne a cikin koda(kidney) da kuma Ureters (hanyar daya sauko da fitsari daga koda) wannan shine infection mafi hadari a ciki.


Kamar yadda muka ce akwai lower track da kuma upper track,haka suma alamomin cutar sun kaso kashi biyu,akwai wanda alamomin na lower track ne akwai kuma alamomin upper track.


ALAMOMIN CUTAR MAFITSARA NA LOWER TRACK.


1. Zafi wajen fitsari

2. Yawan jin fitsari amma idan kaje dan kadan zaka yi 

3. Zaka rika fama da rashin rike fitsari

4. Ganin jini a fitsarin ka

5. Fitsarin ka zai sauka kala kamar cola ko kuma kalar shayi 

6. Fitsari mai wari

7. Ciwon kugu ga mata.

8. Ciwon dubura ga maza


Wadan nan sune Alamomin cutar mafitsara na Lower track,sannan Upper track infection wanda yake a kidney ko ureters yafi hadari da barazana ga rayuwa domin idan bacteria yayi yawa a koda zai shiga jinin ka ya haifar maka da matsala ta karancin jini wanda haka yake kai mutum har lahira.


ALAMOMIN CUTAR MAFITSARA NA UPPER TRACK.


1. Zazzabi

2. Tashin zuciya

3. Amai

4. Jin sanyi a jiki

5. Jin zafi a bangare biyu na baya.


Wadan nan sune Alamomi na cutar mafitsara mafi hadarin kamuwa.


Saboda haka yan uwa ku dena bin rudin masu magani barkatai suyi ta ce muku sanyin mara sanyin mara,akwai abinda ya wuce nan,a rika zuwa ganin likita idan cuta tayi tsanani domin gujewa halaka.


Allah yasa mu dace.


Daga dan uwan ku drmaijalalaini 08137482786


Domin karin bayani ko bukatar magani hadadde muna jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist


Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati


SHARE 


No comments