Ciwon hanta wato hepatitis alamomin ciwon hanta da maganin sa Da yawan mutane suna kamuwa da wannan cuta tsawon lokaci tana tare dasu ba tar...
Ciwon hanta wato hepatitis alamomin ciwon hanta da maganin sa
Da yawan mutane suna kamuwa da wannan cuta tsawon lokaci tana tare dasu ba tare da sun gane ko kuma sunji wata alama ba,kuma wannan Lalura ba karamar cuta bace domin tana iya hallaka mutum cikin kankanin lokaci.
Da farko dai Hepatitis B wani nau'in ciwon hanta ne wanda cutar hepatitis B (HBV) ke haifarwa.
Ba kamar sauran cutukan da ake dauka wajen saduwa yake ba, wanda ake kira da Sexual transmitted disease wato(STI) wanda akan iya gane alamun su cikin kankanin lokaci,hi hepatitis b yana iya samun ka na tswon lokaci amma baka san dashi na kuma hepatitis B yana da illa domin yana haifar da kumburin hanta mai haÉ—ari.
Shi wanna virus na hepatitis B ana iya kamuwa dashi ta hanyar haduwar jinin mai lalurar da naka, ko ruwan jikin mutumin da ya kamu da cutar.
Yawancin mutanen da suka kamu da cutar hepatitis B ba zasu ga wata alama ba kwata -kwata.
Ko da mutum ba shi da alamun cutar, kwayar cutar na iya ci gaba da lalata hanta idan ba a yi maganin ta ba.
Wannan shine dalilin da ya sa yana da mahimmanci mutum ya rika ziyartar likita akai -akai (kamar ziyarar lafiya na shekara -shekara) don bincika alamun da yin gwaji.
ALAMOMIN DA MUTUM ZAI IYA JI IDAN YA KAMU DA WANNAN CUTA.
1. Rasin son cin abinci.
2. Yan jin kasalar jiki
3. Yawaitar ƙananan zazzabi
4. Ciwon tsoka da gwiwa da yawan ciwon kai
5. Yawan jin tashin zuciya
6. Yawan amai
7. Fitsarin mutum yakan koma baki mai duhu.
8. Jikin mutum da idon sa ya koma kalar yello.
Wadan nan sune kadan daga Alamomi da mutum zai iya gane ya kamu da wannan cuta,da zarar ka fara jin wasu alamomi daga wadan nan kayi kokari ka tuntubi likati domin a auna ka,asan abinda ke damun ka.
Yaada zaa hada maganin wannan matsala:
1. Garin habbatussauda
2. Garin Tafarnuwa
3. Garin habburrashad
4. Man habbatussauda.
Yadda zaa hada.
Da farko zaa samu garin habba babban chokali guda 4,garin Tafarnuwa Babba chokali daya da rabi,garin habburrashad babban chokali 3 man habbatussauda 60ml zaa hade su waje daya,sannan a kawo zuma tatacciya me kyau liter 2 a hade a ciki a juya sosai.
Zaa rika shan babban chokali 2 da safe 2 da daddare bayan anci abinci na tsawon wata 2 insha Allah zaa samu waraka,bayan an gama sha aje asibiti ahi gwaji.
Allah yasa mu dace.
Rubutawa tare da dorawa daga zauren maijalalaini.com
Daga Alkalamin dan uwan ku drmaijalalaini 08137482786 domin karin bayani ko shawarwari ko bumatar magani hadadde zaku iya tuntubar mu a jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist.
Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati.
SHARE.
No comments