ALAKAR CIWON SUKARI(DIABETES)DA RAUNIN MAZAKUTA Da farko dai ciwon sukari da matsakar erectile dysfunction (ED) abu biyu ne daban, sun saba...
ALAKAR CIWON SUKARI(DIABETES)DA RAUNIN MAZAKUTA
Da farko dai ciwon sukari da matsakar erectile dysfunction (ED) abu biyu ne daban, sun saba tafiya hannu da hannu. ED shine rashin iya tsayar da azzakari a lokacin bukata.
Mazan da ke da ciwon sukari (diabetes type 2) sunfi samun barazanar kamuwa da ED,sannan Namiji dan shekara 45 wanda yake da matsalar raunin mazakuta ana iya samun sa da matsakar sukari (diabetes type 2)
Ciwon sukari yana faruwa lokacin da yawan sukari ke zagayawa cikin jinin ku. Akwai manyan nau'ikan ciwon sukari guda biyu: type da kuma type 2 amma a kaso 100 na masu ciwon kashi 90 ana samun su da type 2 ne,kaso 10 ne ake samun masu type 1.
Haɗin tsakanin ciwon sukari da ED yana da alaƙa da zagayawar jinin ku da tsarin juyayi na jini. Matakan sukari na jini (blood sugar)da ba a sarrafa su sosai ba na iya lalata ƙananan jijiyoyin jini, Lalacewar jijiyoyin da ke sarrafa motsawar jima'i na iya kawo cikas ga ikon mutum na iya tsayar da azzakari lokacin shaawar yin jima'i,Rage jini daga jijiyoyin da suke kai jini na iya taimakawa ga ED.
Akwai dalilai masu haɗari da yawa waɗanda zasu iya ƙara haɗarin ciwon sukari da kuma raunin mazakuta ED. Sune kamar haka:
1. Wanda baya kula na yanayin gunar(blood sugar) suga na jini ba.
2. Yawan damuwa
3. Yawan bacin rai
4. Yawan baƙin ciki
5. cin abinci mara kyau
6. Yawn kiba
7. Shan hayaki
8. Shan barasa mai yawa
9. Matsakar hawan jini
10. Shan magunguna waÉ—anda suke da side effects da raunin mazakuta.
Idan kana bukatar samun kariya daga hadarin ciwon suga ya kamata ka tika yawaita motsa jiki,daidaita tsarin abincin da kake ci,rage shan taba,rashe shan barasa,rage tunani da yawan zama da bacin rai ko damuwa.
Sannan insha Allah ga wadan da suke da wannan lalaura akwai magani da zamu kawo a bayani namu na gaba a wannan zaure mai albarka.
Allah yasa mu dace.
Daga dan uwan ku drmaijalalaini domin karin bayani ko bukatar magani hadadde 08137482786 muna jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati
SHARE
No comments